Football

Real Madrid Sheriff Tiraspol Football Live Score 29 September 2021

Real Madrid Sheriff Tiraspol Football Live Score 29 September 2021

Wasan da Real za ta karbi bakuncin kungiyar ta Moldova shine na 108 da za ta fafata a gasar Zakarun Turai da kungiyoyi daban-daban.

Sai dai karon farko da Real da Sheriff Tiraspol za su kece raini a babbar gasar Zakarun Turai.

Ranar Laraba 15 ga watan Satumba, Sheriff Tiraspol ta doke Shakhtar Donetsk ta Ukraine 2-0, a kuma ranar Real Madrid ta je ta ci Inter Milan 1-0.

Real ta fara gasar Zakarun Turai cikin watan Satumba da Servette ta Switzerland daga nan kungiyar ta Sifaniya ta dunga yin wasanni da dama a gasar har da na hamayya tsakanin manyan kungiyoyin Turai.

Cikin wasannin na Zakarun Turai Real ta fuskanci Bayern Munich sau 26 da kece raini sau 21 da Juventus.

Haka kuma kungiyoyin Jamus Real Madrid tafi fuskanta a wasannin gasar Turai, wadda ta kara da guda 10.

Wasu kungiyoyin da suka shiga sawun masu fafatawa da Real Madrid sun hada da Atalanta da kuma Chelsea a kakar bara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button